Babban Albishir: Mallakan Shafi a ZamaniWeb Ya Zama Kyauta!

Wallafan January 1, 2019. 11:40pm. Na Ahmad Bala. A Sashin Labaran ZamaniWeb

http://zamaniweb.com/administrator/files/19/01/1/zw-view-on-desktop.png

Muna farin cikin shaida maku cewan daga ranar 1 ga watan Janerun wannan sabuwar shekara ta 2019 ZamaniWeb zai kasance kyauta. Mun bude dukkanin shafukan da ke rufe, sannan mun cire "kwanakin gwaji". Ma'ana yanzu za ku iya kirkiran shafukan ku a kyauta har na tsawon lokacin da kuke so, maimakon sai an biya kudin hidiman shafi na shekar-shekara kaman yadda ya ke a baya. Kuma daga yanzu ZamaniWeb zai ci gaba da kasancewa manhajar yanar gizo mai bayar da aiyukan sa a kyauta, da yardan Allah!

Mayar da ZamaniWeb kyauta shi zai kara ba mu daman tabbatar da manufar mu na karfafa gwiwar al'umma musamman na Afrika kan amfani da fasahar sadarwan zamani don samar da ingantacciyar ci gaba.

Muna da tsare-tsare da za su fito nan ba da jimawa ba, a samfurin 1.0 na manhajar, wanda zai ba mutum daman canja tsarin shafin sa daga "Tsari Na Kyauta" zuwa "Tsari Na Biya" a duk lokacin da ya bukaci yin hakan. Ta yadda duk mai bukatan karin aiyuka a shafin sa zai iya biyan kudi domin komawa babban tsarin, wato tsarin da za a rika biya shekara-shekara, mai kunshe da wasu karin aiyuka na mussamman.

Har yanzu dai ZamaniWeb jaririn manhaja ne wanda Ahmad Bala ke ci gaba da assasawa da-sannu-da-sannu. Fatan mu shi ne manahajar ya zama abin alfahari ba ma ga masu amfani da harshen Hausa kadai ba har ma ga dukkan mutanen nahiyar Afrika. Muna godiya da kwarin gwiwa da shawarwarin da muke samu daga gare ku.

Bissalam, mu huta lafiya..!!


Tura wannan zuwa:

An yi sharhi 5 a kan "Babban Albishir: Mallakan Shafi a ZamaniWeb Ya Zama Kyauta!"


Babu hoto23-01-2019
ali ibrahim bakaro

naji dadin ganin ku amma ina da tambayoyi da nake son ku taimake ni a kansu


Babu hoto26-01-2019
Ahmad Bala

@ali ibrahim bakaro, muna jin ka, kana iya yin tambayoyin ka a nan ko kuma ka aiko mana sako ta Email: admin@zamaniweb.com


Babu hoto06-08-2019
Mudassir Abdulrahaman Gulu

Gaskiya nayi farin ciki sosai da irin Wannan tagomashi muna Godiya Allah ya kara daukaka.


Babu hoto30-08-2019
Salisu

SLM tambayata itace da Allah ana iya aikawa da audio kokuma bidiyo ashafin da aka kirkira a zamaniweb bissalam


Babu hoto16-09-2019
Ahmad Bala

@Salisu Eh, kwarai kuwa! Ana iyawa.

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Game Da ZamaniWeb

ZamaniWeb manhajar yanar gizo ne da ke bayar da daman kirkiran shafin yanar gizo a harshen Hausa, cikin sauki. Za ku iya kirkiran shafin yanar gizo ko kuma blog kaman wannan a ZamaniWeb.com domin amfanin al\'ummar ku ko kuma domin bunkasa harkokin kasuwancin ku a zamanance. Ku ziyarci www.zamaniweb.com a yanzu domin mallakan naku shafin yanar gizon a kyauta!


Amfani da ZamaniWeb babu wahala!

Amfani da manhajar yanar gizon ZamaniWeb abu ne mai sauki. A duk lokacin da ka bukaci gudanar da gyare-gyare ko wallafa bayanai a shafin ka, kawai sai ka shiga cikin taskan ka na ZamaniWeb ta hanyar amfani da lakabi da kalman sirrin da ka yi rajista da su, sai ka zabi "Shiga sashin sarrafa shafin".


Kasidu Masu Alaka