Gabatarwa Da Sharhi Game Da ZamaniWeb Daga Wanda Ya Kirkira

Wallafan March 9, 2018. 9:00am. Na Ahmad Bala. A Sashin Labaran ZamaniWeb

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/03/1/dsc02961-new.jpg

Assalamu alaikum, jama'a barkan mu da war haka. Suna na Ahmad Bala, jagora kuma wanda ya kirkiro ZamaniWeb. Ina farin cikin gabatar ma ku da wannan sabuwar fasaha na kirkiran shafin yanar gizo, wato ZamaniWeb.

A shekarun baya, mallakan shafin yarnar gizo ya kasance abu ne mai wahala wanda hakan ya sanya aka bar masu kananan sana'o'i da kamfanoni masu tasowa a baya wajen cin moriyar amfani da fasahar yanar gizo wajen bunkasa harkokin cinikayya.

A da, idan mutum na son samun shafin yanar gizo, to sai dai ya nemi maginin shafin yanar gizo wato "web designer" ko "web developer" domin ya gina ma sa, wanda dole sai ya caje shi kudi masu yawa kuma dole sai ya jira na 'yan wasu kwanaki kafin a kammala aikin gina ma sa shafin. Idan kuma ya na so ya kirkira da kan sa ne, to sai dai ya yi amfani da "website builders" na kasashen waje irin su Weebly ko Wordpress ko blogger da sauran su, wanda duk basu bayar da daman kirkiran shafi cikin harsunan mu na Afrika irin su Hausa ko Yarbanci da sauran su, sannan mafi yawancin su su na da wuyan sarrafawa. Idan kuma dan karamin website na waya mutum ke so ya kirkira, to sai dai ya nemi Nextwapblog wanda gaba dayan sa cikin harshen Indonesia ya ke, ko irin su xtgem ko Wapka wanda su kuma sai sun rika sako tallace-tallacen su a shafin da mutum ya kirkira tare da manhajar su.

Hakan ne ya sa na ga cewan lallai, ya kamata mu fara samar da na mu manhajar a cikin harsunan mu na Afrika, wanda zai kasance mai saukin sarrafawa ga kowa, kuma wanda za a iya bude shi a duk wayoyin hannu da kuma manya da kananan kwamfutoci. Domin hakika, lokaci ya yi da yakamata a ce mun fara amfani da hikima da fasahar da Allah Ya ba mu wajen kirkiran abubuwan da za su amfane mu, ba kawai mu jira sai wasu sun kirkiri ba sannan mu yi amfani da su.

A matsayi na na mai sana'ar gina shafukan yanar gizo, kuma injiniyan manhajar yanar gizo mai zaman kan sa, na shafe watanni da dama ina gina wannan manhaja na ZamaniWeb. Kuma hakika ina godiya ga Allah da ya ba ni ikon jajircewa tare da yin aiki tukuru don kirkiro wannan fasaha wanda na tabbata zai taimaki dimbin al'umma. Na yi bincike-bincike da nazari mai yawa a game da yadda fasahar yanar gizo ke aiki don tabbatar da cewan manhajar ZamaniWeb ya kasance ingantacce wanda ke tafe da fasahohin zamani wadanda ake yayi a duniyan a halin yanzu, kuma tare da dubi da abubuwan da mu ka fi bukata a kasashen mu na Afrika, da kuma yanayin karfin sadarwan Intanet wanda a kan samu bambacin sa a tsakanin yankuna.

Hakika, ZamaniWeb ya zo domin canja yadda mu ke tunani game da samun shafin yanar gizo. ZamaniWeb ya kawo sauki musamman ma ga masu sana'o'in hannu a halin yanzu, kaman mai sana'ar kwalliya da mai sana'ar daukan hoto da masu gidan abinci da masu shagon saye da sayarwa, da sauran sana'o'i. Komai girma ko kankantar kasuwancin da mutum ke yi, zai iya mallakan dan matsakaicin shafin yanar gizon sa ta hanyar ZamaniWeb, wanda zai ishe shi bunkasa harkokin cinikayyan sa da kuma sadarwa tsakanin sa da abokan huldan sa cikin sauki kuma a zamanance.

Da ZamaniWeb, za ku iya kirkiran nau'uka daban-daban na shafin yanar gizo, kaman na kasuwanci ko na kungiya ko kuma kawai na amfanin-kai, don wallafa aiyukan ku na kirkire-kirkire da adabi da sauran al'amuran rayuwa na yau-da-kullum.

A halin yanzu, samfurin farko na manhajar ne za ku gani (version 0.9). Wannan samfurin na ZamaniWeb V.0.9 na bayar da daman kirkiran shafin yanar gizo wanda ke da bangarori uku; bangaren farko, wanda shi zai ba ka daman saka tsayayyun bayanai da hotuna game da shafin. Sai kuma bangaren blog wanda zai ba ka daman wallafa rubuce-rubuce ko kasidu a-kai-a-kai wanda za su iya kunsan hotuna da fayilolin PDF, MS word, da MS excel. Sai kuma bangare na uku wanda shi ne bangaren "tuntuba", zai bai wa maziyarta shafin ka daman tuntubar ka ta hanyar cike fom a shafin na ka.

Samfurin manhajar na biyu (ZamaniWeb version 1.0) wanda ke tafe, shi ne zai kasance cikakke, wanda zai kunshi karin sauran abubuwa da tsare-tsaren da babu su a yanzu, da yardan Allah.

Ina godiya ga dukkan wadanda su ka yi rajista kuma su ka kirkiri shafukan su da ZamaniWeb, da wadanda su ke da niyyar yin hakan.

A yayin da za ku ci gaba da more wa amfani da manhajar, kada ku manta, ku taya mu yada wannan albishir, ku sanar da 'yan'uwa da abokan ku game da ZamaniWeb.

Sai an jima, ku huta lafiya!


Tura wannan zuwa:

An yi sharhi 3 a kan "Gabatarwa Da Sharhi Game Da ZamaniWeb Daga Wanda Ya Kirkira"


Babu hoto20-07-2018
Ambdauran

Godiya ta musanman wa admin na zamaniweb fatan Allah yakara muna fasaha


Babu hoto31-07-2018
Ahmad Bala

Amin! Godiya gare ka kai ma @Ambdauran


Babu hoto05-09-2019
EllEdgesk

Acquistare Sildenafil 100 Milligrammi Amoxicillin And Chewable Tablets Acheter Tadalis Sx 40 Mg cialis without prescription Cialis Duree Traitement Propecia Work Long Term

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Game Da ZamaniWeb

ZamaniWeb manhajar yanar gizo ne da ke bayar da daman kirkiran shafin yanar gizo a harshen Hausa, cikin sauki. Za ku iya kirkiran shafin yanar gizo ko kuma blog kaman wannan a ZamaniWeb.com domin amfanin al\'ummar ku ko kuma domin bunkasa harkokin kasuwancin ku a zamanance. Ku ziyarci www.zamaniweb.com a yanzu domin mallakan naku shafin yanar gizon a kyauta!


Amfani da ZamaniWeb babu wahala!

Amfani da manhajar yanar gizon ZamaniWeb abu ne mai sauki. A duk lokacin da ka bukaci gudanar da gyare-gyare ko wallafa bayanai a shafin ka, kawai sai ka shiga cikin taskan ka na ZamaniWeb ta hanyar amfani da lakabi da kalman sirrin da ka yi rajista da su, sai ka zabi "Shiga sashin sarrafa shafin".


Kasidu Masu Alaka