Ko Kun San Me Ake Nufi Da Spam Bot?

Wallafan January 17, 2021. 2:54pm. Na Ahmad Bala. A Sashin Darussan ZamaniWeb

Mutum-tumin yanargizo!

Spam bot mutum-mutumi ne amma na yanargizo wanda wasu mutane kan kirkira domin cin ma wata manufa tasu ta lalata tsari ko kuma sace bayanan sirri a shafukan yanargizo. Shi spam bot zai rika gudanar da wasu aiyuka ne a kan shafi tamkar yadda dan'adam zai yi. Zai shiga shafi, ya cike fom, har ma ya wallafa sharhi wato comment. Wasu nau'ukan kuma, sace bayanai kawai suke yi, da zaran sun shiga shafi, sai su duba idan akwai lambobin waya ko adireshin Email sai su kwafe, su tura wa mutumin da ya kirkire su.

A takaice dai, Spam bot manhaja ne wato software da akan kirkire shi da fasahohi irin su JavaScript, domin ya yi aikin kutse ko satar bayanai daga shafukan yanargizo kai-tsaye.

Akwai nau'ukan spam bot daban-daban, amma fitattu guda biyu su ne:

  1. Spam bot na Email
    Shi wannan shi ne wanda yake aika sakonnin Email marasa ma'ana ko kuma sakonnin Email na yaudara masu kunshe da mahadan satar bayanai, zuwa ga akwatin sako na adireshin Email din dubban mutane a lokaci guda. Mafi yawancin irin wadannan sakonnin su ne za ka gan su a cikin kundin 'Spam' ko 'Junk mails' idan ka bude Email din ka.
  2. Spam bot na Shafin yanargizo
    Shi wannan shi ne mai bibiyan shafukan yanargizo domin sace bayanan sirri ta hanyar cike duk wani fom da ya ci karo da shi a shafin kai-tsaye. Shi ne ya sanya za ku ga a shafukan blog ana samun wasu masu yin 'comment' maras ma'ana, to irin wannan comment ba mutane ne ke yin su ba, mutum-mutumin yanargizo ne.

http://zamaniweb.com/administrator/files/21/01/1/spambot-mutummutumin-yanargizo.png

Wane hanya ake bi domin tsare shafukan yanargizo daga Spam bot?

Hanya mafi shahara da ake bi wajen tsare shafukan yanargizo daga irin wadannan spam bots shi ne sanya 'hoton tantancewa' wanda a turance ake kira da "Completely Automated Public Turing test to tell Computers and Humans Apart" (CAPTCHA). Wani dan hoto ne wanda ke dauke da alamomin haruffa gami da lambobi a lankwashe ko a soke, wanda sai mutum ya cike su kafin ya wallafa sharhi ko kuma aika fom a shafin yanargizo. Fahimtar alamomin da ke jikin irin wannan hoton kan yi wa spam bot wahala, don haka ake sanya shi a shafukan yanargizo domin yin maganin sa.

To ya zan yi in saka Alamar tantancewan wato CAPTCHA a shafin blog dina na ZamaniWeb?

Idan ka shiga taskan ka na ZamaniWeb, ka "Shiga masarrafar shafin", sai ka shiga bangaren "Canja Saice-saicen Shafi".

A wajen "Canja Saice-saicen shafi" za ka ga inda aka sa "A saka tsaro (hoton tantancewa) a fom?" sai ka zabi "Eh" sannan sai ka je kasa ka latsa "Sabunta Saitin".

Shi ke nan!

A sani cewa: idan ba ka sa hoton tantancewan a shafin ka ba akwai yiyuwar za ka rika ganin spam bot yana wallafa maka dubban sharhi marasa ma'ana a shafin ka, wanda hakan zai iya sanya shafin ka ya rika yin nauyi wajen budowa. Idan shafin ka ya yi nauyi da yawa kuma, shafin zai samu cikas wajen bayyana a sakamakon binciken Google search.

Domin tabbatar da cikakken tsaro da inganci ga shafukan ku na ZamaniWeb, mun sanya manhajar mu ya saka hoton tantancewan kai-tsaye ga duk wani sabon shafin da za ku kirkira daga yanzu. Amma idan mutum ba ya bukata, sai ya je bangaren saice-saicen shafin sa ya cire ta hanyar zaban "A'a".


Tura wannan zuwa:

Kasance na farko wajen yin sharhi a kan "Ko Kun San Me Ake Nufi Da Spam Bot?"

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Game Da ZamaniWeb

ZamaniWeb manhajar yanar gizo ne da ke bayar da daman kirkiran shafin yanar gizo a harshen Hausa, cikin sauki. Za ku iya kirkiran shafin yanar gizo ko kuma blog kaman wannan a ZamaniWeb.com domin amfanin al\'ummar ku ko kuma domin bunkasa harkokin kasuwancin ku a zamanance. Ku ziyarci www.zamaniweb.com a yanzu domin mallakan naku shafin yanar gizon a kyauta!


Amfani da ZamaniWeb babu wahala!

Amfani da manhajar yanar gizon ZamaniWeb abu ne mai sauki. A duk lokacin da ka bukaci gudanar da gyare-gyare ko wallafa bayanai a shafin ka, kawai sai ka shiga cikin taskan ka na ZamaniWeb ta hanyar amfani da lakabi da kalman sirrin da ka yi rajista da su, sai ka zabi "Shiga sashin sarrafa shafin".


Kasidu Masu Alaka