Me Ake Nufi Da Tsaftataccen Adireshi a Yanargizo?

Wallafan November 19, 2019. 5:57pm. Na Ahmad Bala. A Sashin SEO don shafin ku

http://zamaniweb.com/administrator/files/19/11/1/tsaftataccen-adireshi-clean-url.jpg

Tsaftataccen adireshi abin da a turance ake kira "clean URL" shi ne adireshi shafin yanar gizo wanda ba ya nuna nau'in fasahar da aka yi amfani da shi wajen gina shafin.

Misali: https://zamaniweb.com/administrator/shafin-shiga (tsaftatacce) maimakon https://zamaniweb.com/administrator/shafin-shiga.php (wanda ba tsaftatacce ba).

Idan kuka dubi misalin da kyau za ku lura akwai karin ".php" a wanda ba tsaftataccen ba. Abin da ke nuna cewa wato an yi amfani da fasahar PHP kenan wajen gina shafin.

To Mene Ne Hikimar Samar Da Tsaftataccen Adireshin?

(1) Tsaftataccen adireshi ya fi saukin rubutawa da kuma haddacewa. Idan adireshin shafin ka tsaftatacce ne, mutane za su fi saurin tuna shi. Ba sai sun tsaya suna rubuta wani .php ko .html a karshen adireshin ba. Kawai da zaran sun rubuta taken adireshin shafin, zai bude kai tsaye.

(2) Tsaftataccen adireshi shi ne ake yayi a duniyar fasahar yanargizo. Wancan salon na samar da adireshi mai nuna fasahar da aka yi amfani da shi, ya zama tsohon yayi.

(3) Tsaftataccen adireshi yana kara saukaka SEO ("search engine optimization) na shafin ka, ma'ana, shafin ka zai samu wani tagomashi na musamman a shafukan bincike-bincike irin su Google da makamantan sa. Domin su shafukan bincike-binciken sun fi son shafukan yanargizo masu tsaftataccen adireshi. Hakan ne ma ya sa a wasu lokutan akan kira tsaftataccen adireshi da "Search engines friendly URL" wato adireshin da ya fi soyuwa ga shafukan bincike-bincike.

Albishirin Ku!

Dukkan adireshin shafukan yanar gizon da aka kirkira ta hanyar manhajar mu na ZamaniWeb tsaftataccen adireshi ne. Dukkan shafukan ku suna tare ne da tsaftataccen adireshi matukar a ZamaniWeb kuka kirkiri shafin.

Misali: http://www.ahmadbala.zamaniweb.com/blog

Wannan na daya daga cikin abubuwan da suka sanya manhajar ZamaniWeb ya tsere wa tsara!


Tura wannan zuwa:

Kasance na farko wajen yin sharhi a kan "Me Ake Nufi Da Tsaftataccen Adireshi a Yanargizo?"

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Game Da ZamaniWeb

ZamaniWeb manhajar yanar gizo ne da ke bayar da daman kirkiran shafin yanar gizo a harshen Hausa, cikin sauki. Za ku iya kirkiran shafin yanar gizo ko kuma blog kaman wannan a ZamaniWeb.com domin amfanin al\'ummar ku ko kuma domin bunkasa harkokin kasuwancin ku a zamanance. Ku ziyarci www.zamaniweb.com a yanzu domin mallakan naku shafin yanar gizon a kyauta!


Amfani da ZamaniWeb babu wahala!

Amfani da manhajar yanar gizon ZamaniWeb abu ne mai sauki. A duk lokacin da ka bukaci gudanar da gyare-gyare ko wallafa bayanai a shafin ka, kawai sai ka shiga cikin taskan ka na ZamaniWeb ta hanyar amfani da lakabi da kalman sirrin da ka yi rajista da su, sai ka zabi "Shiga sashin sarrafa shafin".


Kasidu Masu Alaka