Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata a Sani Game Da ZamaniWeb

Wallafan March 17, 2018. 7:20pm. Na Ahmad Bala. A Sashin Darussan ZamaniWeb

• ZamaniWeb manhajar yanar gizo ne da ke bayar da daman kirkiran shafin yanar gizo a harshen Hausa, cikin sauki.

• Yanzu za ku iya mallakan tsararren shafin yanar gizon ku don bunkasa harkokin kasuwancin ku ko kamfanin ku ko kungiyar ku ko kuma kawai don amfanin-kai.

• Matukar dai mutum na da adireshin Email kuma zai iya shiga cikin Email din don karanta sako, to zai iya mallakan shafin yanar gizo a ZamaniWeb.

• Babu bukatar sai ka nemi wani masani ko maginin shafin yanar gizo. Babu bukatar sai ka mallaki kwamfuta ko iya sarrafa kwamfuta. A ZamaniWeb za ka iya kirkiran shafin yanar gizon ka da wayar ka ta hannu a yayin da ka ke kwance a kan gadon dakin ka.

• An kirkiro ZamaniWeb ne domin saukaka hanyar mallakan shafin yanar gizo ga mutanen Afrika.

• An kirkiri ZamaniWeb ne a cikin harshen Hausa zalla, don bunkasa amfani da harshen da kuma karfafa gwiwan al'umma kan amfani da harsunan gida na Afrika a wajen kirkire-kirkire a fannin fasahar sadarwan zamani, don samar da ingantaccen ci gaba mai dorewa.

• Matakai 4 ne masu sauki kawai za ka bi domin mallakan sabon shafin yanar gizon ka a yanzu, a ZamaniWeb:

1. Matakin farko shi ne yin rajista, wato bude sabon taska a ZamaniWeb.
2. Mataki na biyu shi ne tantance adireshin Email din da aka yi rajistan da shi.
3. Mataki na uku shi ne shiga cikin taskan, wato "Login".
4. Mataki na hudu shi ne kirkiran sabon shafin yanar gizon.

• Yin rajistan har zuwa kirkiran shafin duk kyauta ne. Babu bukatan sai ka biya ko sisi. Kuma bai wuce ya dauke ka mintuna 3-5 ba.

• A lokacin da ka kirkiri sabon shafin yanar gizon ka a ZamaniWeb, manhajar mu zai kirkiri adireshin shafin ka mai saukin fada da yadawa kaman: www.taken-shafin.zamaniweb.com kai tsaye, kuma a nan take kuma duk a kyauta. Wannan na nufin cewan daga lokacin da ka kirkiri sabon shafin yanar gizon ka nan take kowa zai iya ziyartan shafin.

• Shafin da ka kirkira zai iya kasancewa a harshen Hausa ko kuma turanci (English). Ma'ana za ka samu daman sauya yaren shafin da ka kirkira din daga Hausa zuwa Ingilishi ko kuma daga Ingilishi zuwa Hausa a duk lokacin da ka so yin hakan.

• Shafin da ka kirkira zai kasance yana da bangaren blog inda za ka rika wallafa rubuce-rubucen ka da hotuna. Sannan akwai kuma bangaren "Tuntuba" inda maziyarta shafin ka za su samu daman tuntubar ka ta hanyar cike fom a shafin naka.

• Maziyarta shafin ka za su samu daman wallafa sharhi ("comment") a karkashin rubuce-rubucen ka ko kasidu na bangaren blog. Za ka iya rufewa da kuma bude daman yin sharhin a ko da yaushe. Sannan za ka iya goge sharhin da ba ka so, duk a sashin sarrafa shafin ka.

• Za ka samu sanarwa ("notification") a sashin sarrafa shafin ka a duk lokacin da wani maziyarcin shafin ka ya wallafa sharhi a shafin naka.

• Za ka iya canja jimillan launin shafin ka ("Colour theme") a ko da yaushe, a sashin sarrafa shafin ka. Domin kalan shafin ka ya kasance dai-dai da kalan kasuwancin ka ko kamfanin ka.

ZamaniWeb dashboard

• A duk lokacin da ka bukaci gudanar da gyare-gyare ko wallafa bayanai a shafin ka, kawai sai ka shiga cikin taskan ka na ZamaniWeb ta hanyar amfani da Lakabi ("username") da mabudin sirrin ("password") da ka yi rajista da su, sai ka zabi "Shiga sashin sarrafa shafin".

• Ana samun daman kirkiran shafukan yanar gizo iri daban-daban har guda biyar a karkashin taskan da aka yi rajista.

• Komai girma ko kankantar sana'ar ka ko kasuwancin ka ko kamfanin ka, za ka iya mallakan matsakaicin shafin yanar gizon ka a ZamaniWeb, wanda zai ishe ka bunkasa harkokin cinikayyan ka da kuma isar da sakonni zuwa ga abonkan cinikayyan ka a zamanance, a wannan sabuwar duniya da muke ciki na Intanet.

• Mallakan shafin yanar gizo shi ne babban hanya na bunkasa harkokin kasuwanci da kuma kulla alaka da abokan cinikayya a zamanin yanzu. Don haka kada ku bari wannan dama ta wuce ku. Kirkiri shafin yanar gizon ku yanzu, a ZamaniWeb.

• Shiga www.zamaniweb.com

• An kirkiri ZamaniWeb ne a cikin harshen Hausa zalla, don bunkasa amfani da harshen da kuma karfafa gwiwan al'umma kan amfani da harsunan gida na Afrika a wajen kirkire-kirkire a fannin fasahar sadarwan zamani, don samar da ingantaccen ci gaba mai dorewa.

Domin karin bayani game da matakai guda 4 da ake bi don kirkiran sabon shafin yanar gizo a ZamaniWeb, sai a > latsa nan.

Tura wannan zuwa:

An yi sharhi 2 a kan "Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata a Sani Game Da ZamaniWeb"


Babu hoto06-04-2018
Ambdauran

Muna godiya da chanjin da akasamu awannan shafin


Babu hoto06-04-2018
Ambdauran

Muna godiya da chanjin da akasamu awannan shafin

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Game Da ZamaniWeb

ZamaniWeb manhajar yanar gizo ne da ke bayar da daman kirkiran shafin yanar gizo a harshen Hausa, cikin sauki. Za ku iya kirkiran shafin yanar gizo ko kuma blog kaman wannan a ZamaniWeb.com domin amfanin al\'ummar ku ko kuma domin bunkasa harkokin kasuwancin ku a zamanance. Ku ziyarci www.zamaniweb.com a yanzu domin mallakan naku shafin yanar gizon a kyauta!


Amfani da ZamaniWeb babu wahala!

Amfani da manhajar yanar gizon ZamaniWeb abu ne mai sauki. A duk lokacin da ka bukaci gudanar da gyare-gyare ko wallafa bayanai a shafin ka, kawai sai ka shiga cikin taskan ka na ZamaniWeb ta hanyar amfani da lakabi da kalman sirrin da ka yi rajista da su, sai ka zabi "Shiga sashin sarrafa shafin".


Kasidu Masu Alaka