Samu Bayanan Kididdiga Game da Cutar Korona Bairos (Covid-19)

Wallafan April 5, 2020. 6:02pm. Na Ahmad Bala. A Sashin Labaran ZamaniWeb

Assalamu alaikum,

Jama'a ya muka ji da alhinin shigowan wannan annoba ta korona bairos? To, muna fatan kowa na lafiya. Allah Ya sa haka, Amin.

Muna kara tunasar da jama'a a kan daukan duk matakan da suka dace domin kare kai daga kamuwa da wannan cuta. Tare da bin dukkanin umarnin da hukumomi suka bada da kuma shawarwarin da masana kiwon lafiya ke bayarwa domin dakile yaduwar wannan cuta. Haka kuma, kada mu manta da rokon Allah.

ZamaniWeb ya tanadar maku da shafi na musamman inda za ku rika samun bayanan kididdiga kai tsaye game da wannan cuta ta Korona bairos, na kowace kasa a fadin duniya.

bayanan-kididdiga-game-da-covid19-a-hausa.png

Adireshin shafin shi ne: https://zamaniweb.com/bayanai/covid19

Da zaran kun budo shafin, sai ku zabi sunan kasar da kuke son samun kididdigan ta, nan take za ku samu.

A halin yanzu, shafin yana aiki ne ga masu amfani da kwamfuta (desktop ko laptop) kadai. Amma ba da jimawa ba za ku iya fara dubawa a wayoyin ku da yardan Allah. Muna kokarin sabunta shafin kai tsaye, kuma akai-akai, da sababbin bayanan kididdigan daga hukumomin da ke tattara bayanan na kasashe daban-daban. Muna maraba da dukkanin ra'ayoyin ku da shawarwarin ku a kan wannan. Tare da fatan za a amfana, kuma za a ci gaba da kokarin kiyaye kai daga kamuwa da wannan cuta.

Sannan kada ku manta: Idan ku na dauke da wasu bayanai da kuke ganin za su taimaki al'umma musamman wajen kare kan su daga kamuwa da wannan cuta, za ku iya bude shafin yanargizon ku a ZamaniWeb, domin wallafa bayanan naku a kyauta.

Ni ne naku Ahmad Bala, ke cewa mu zama lafiya! Allah Ya kiyaye mu da kiyayewar Sa. Amin.


Tura wannan zuwa:

An yi sharhi 2 a kan "Samu Bayanan Kididdiga Game da Cutar Korona Bairos (Covid-19)"


Babu hoto09-06-2020
Musa Ibrahim

ALLAH yasa mudace


Babu hoto10-06-2020
Ahmad Bala

Ameen @Musa Ibrahim

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Game Da ZamaniWeb

ZamaniWeb manhajar yanar gizo ne da ke bayar da daman kirkiran shafin yanar gizo a harshen Hausa, cikin sauki. Za ku iya kirkiran shafin yanar gizo ko kuma blog kaman wannan a ZamaniWeb.com domin amfanin al\'ummar ku ko kuma domin bunkasa harkokin kasuwancin ku a zamanance. Ku ziyarci www.zamaniweb.com a yanzu domin mallakan naku shafin yanar gizon a kyauta!


Amfani da ZamaniWeb babu wahala!

Amfani da manhajar yanar gizon ZamaniWeb abu ne mai sauki. A duk lokacin da ka bukaci gudanar da gyare-gyare ko wallafa bayanai a shafin ka, kawai sai ka shiga cikin taskan ka na ZamaniWeb ta hanyar amfani da lakabi da kalman sirrin da ka yi rajista da su, sai ka zabi "Shiga sashin sarrafa shafin".


Kasidu Masu Alaka