Darasi a Kan Adireshin Shafin Yanargizo (website address/URL)

Wallafan November 2, 2020. 12:28pm. Na Ahmad Bala. A Sashin Darussan ZamaniWeb

Kamar yanda kuka san cewa kowane gida yana da adireshi, haka ma kowane shafin yanargizo na da adireshin sa, wanda zai kasance babu wani shafi mai irin wannan adireshin a duniya sai shi. Adireshin shafi na da matukar muhimmanci cikin al'amuran mallakan shafin yanargizo. Don haka wajibi ne a fahimci mene ne shi, kuma a san yadda ya ke. A wannan darasin na kawo cikakken bayani game da adireshin shafin yanargizo, cikin salon tambaya da amsa, a gajarce, don saukaka fahimta a hausance. Da fatan za a karanta cikin natsuwa. Abin da ba a fahimta ba, ana iya wallafa tambaya a bangaren sharhi da ke kasan wannan bayanin.

Mene ne adireshin shafi?

Adireshin shafin yanargizo wato 'web address' ko kuma URL a turance. Shi ne abin da za a rubuta a kan manhajar shiga yanargizo wato browser domin budo shafi. Kowane shafin yanargizo yana da adireshin sa na musamman wanda babu wani mai irin sa a duk duniya. Galibi adireshin shafi yana farawa ne da 'www' amma akwai wasu shafukan wanda akan sanya adireshin shafin su ba tare da wannan www din ba.
Misali: www.zamaniweb.com ko kuma kawai zamaniweb.com

To mene ne 'http://' ko kuma 'https://' ??

Shi wannan shi ne ke zuwa a farkon kowane adireshin shafin yanargizo. Amma babu bukatar sai an rubuta shi a yayin budo wani shafi. Domin manhajar browser din ya riga ya san da shi, zai sanya shi kai-tsaye. Shi aikin wannan 'http://' shi ne ya sadar da ma'adanar shafin wato 'web server' tare da kwamfutar ka ko wayar ka, ta yadda dukkanin bayanan da aka adana na shafin zai sauka a kan kwamfutar ko wayar taka. Kuma bambanci tsakanin 'http://' da 'https://' shi ne harafin 's' wanda ke nufin 'secure'. Wato idan kaga 'https://' to akwai cikakken tsaro kenan a sadarwan da ke tsakanin browser din ka da ma'adanar shafin.

To me ake nufi da Taken Adireshi?

Taken adireshin shafi shi ne abin da a turance ake kira 'domain name'. Shi ne ainahin kalma ko haruffan da adireshin ya kunsa. Kuma yana karewa ne da wasu haruffa da ake kira 'domain name extension' wanda su ne irin su '.com' da '.org' da '.net' da '.ng' da dai sauran su. Shi taken adireshin yin rajistan sa ake yi a shafukan kamfanonin da ke bada rajistan wanda su ne ake kira 'domain name registrars'. Yin rajistan ba kyauta ba ne. Kuma kowane kamfanin da ke yin rajistan na da nasa farashin da ya ke caji na kowane nau'in taken adireshi. Amma akwai wasu kamfanonin da ke bayar da daman yin rajistan wasu nau'uka na taken adireshin a kyauta.

Shi Taken adireshin yana da bangarori nawa ne?

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/11/1/parts-of-domain-name-1024x536.jpg

Taken adireshi yana da bangarori ko matakai guda uku:

  • Mataki na uku (third-level domain): Wannan shi ake kira 'Subdomain'. Shi ne ke zuwa a farkon adireshin. Kuma ya kan iya kasancewa shi ne 'www' din a wani adireshin. Ko kuma su zo tare da www din.
  • Mataki na biyu (second-level domain): Wannan shi ne jigon taken adireshin don haka shi ake kira 'Domain'. Shi ya kan kasance a tsakiyan adireshin shafi.
  • Babban mataki (top-level domain): Wannan shi ake kira 'domain name extension' din. Shi ne ke zuwa a karshen adireshin.

Nau'ukan taken adireshi guda nawa ne?

Bisa la'akari da bangarorin taken adireshin, za mu iya kasa taken adireshi zuwa gida biyu kamar haka:

  1. Taken adireshin da ya hada bangaren mataki na biyu da bangaren babban mataki, shi ne ake kira 'Domain web address' a turance. Ga misalin sa: zamaniweb.com
  2. Taken adireshin da ya hada duka bangarorin; wato bangaren mataki na uku da bangaren mataki na biyu da bangaren babban mataki, shi ne ake kira 'Sub-domain web address' a turance. Ga misalin sa: suna.zamaniweb.com

To wane irin nau'in taken adireshin shafi ZamaniWeb ke badawa, kuma nawa ne farashin sa a ZamaniWeb?

ZamaniWeb na bayar da daman mallakan shafin yanargizo a kyauta kuma tare da adireshin shafin a kyauta. Nau'in taken adireshin shafin da ke zuwa tare da shafin na kyauta shi ne nau'in taken adireshi na biyu (sub-domain web address) wanda na yi bayani a sama. Wato misali: suna.zamaniweb.com

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/11/1/adireshin-shafi-kyauta-a-zamaniweb.png

Idan ka kirkiri shafin ka a ZamaniWeb, rajistan adireshin shafin ka zai kasance yana tare ne da rajistan adireshin manhajar yanargizon mu na ZamaniWeb. Don haka babu bukatar sai ka biya kudi ga kamfanonin da ke rajistan adireshin don samun taken adireshin ka. ZamaniWeb ya hutashshe ka yin wannan.

To idan kuma ina bukatar taken adireshi mai nau'i na farkon fa?

Idan kana bukatar taken adireshi mai nau'i na farko (domain web address) wanda na yi bayani a sama, wato a misali; kana so ya kasance kawai: suna.com to sai ka ziyarci shafukan daya daga cikin kamfanonin da ke yin rajistan adireshin shafi, ka sayo irin wannan adireshin, sannan sai ka zo ka hada shi da shafin da ka kirkira a ZamaniWeb. Akwai karin bayani na musamman da za mu kawo game da wannan insha'Allah!


Tura wannan zuwa:

An yi sharhi 8 a kan "Darasi a Kan Adireshin Shafin Yanargizo (website address/URL)"


Babu hoto12-11-2020
Abdullahi Usman

madallah da wannan bayanin naka muna sauraron Karin bayanin mungode


Babu hoto17-12-2020
HAMZAUSMAN

AGASKIYA MUNGODE ALLAH YABIYAKU


Babu hoto20-12-2020
Usman Gangkuba Binyeri

Muna Godiya Kuma Muna Jiran Karin Bayani.


Babu hoto17-01-2021
ezesmunuginat

http://mewkid.net/when-is-xuxlya2/ - Amoxicillin 500mg Buy Amoxicillin rpc.dflg.official.zamaniweb.com.mxq.at http://mewkid.net/when-is-xuxlya2/


Babu hoto17-01-2021
uwizuqa

http://mewkid.net/when-is-xuxlya2/ - Buy Amoxicillin Buy Amoxicillin rxy.yswa.official.zamaniweb.com.jvm.fe http://mewkid.net/when-is-xuxlya2/


Babu hoto17-01-2021
uaiduymaag

http://mewkid.net/when-is-xuxlya2/ - Amoxicillin 500mg Buy Amoxicillin Online Without Prescription oig.eirh.official.zamaniweb.com.icp.od http://mewkid.net/when-is-xuxlya2/


Babu hoto08-02-2021
egadova

http://mewkid.net/when-is-xuxlya3/ - Amoxicillin Online Buy Amoxicillin Online azd.lzok.official.zamaniweb.com.lss.ji http://mewkid.net/when-is-xuxlya3/


Babu hoto08-02-2021
oruwequkoc

http://mewkid.net/when-is-xuxlya3/ - Amoxicillin 500mg Amoxicillin 500 Mg yva.oodd.official.zamaniweb.com.jbj.mw http://mewkid.net/when-is-xuxlya3/

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Game Da ZamaniWeb

ZamaniWeb manhajar yanar gizo ne da ke bayar da daman kirkiran shafin yanar gizo a harshen Hausa, cikin sauki. Za ku iya kirkiran shafin yanar gizo ko kuma blog kaman wannan a ZamaniWeb.com domin amfanin al\'ummar ku ko kuma domin bunkasa harkokin kasuwancin ku a zamanance. Ku ziyarci www.zamaniweb.com a yanzu domin mallakan naku shafin yanar gizon a kyauta!


Amfani da ZamaniWeb babu wahala!

Amfani da manhajar yanar gizon ZamaniWeb abu ne mai sauki. A duk lokacin da ka bukaci gudanar da gyare-gyare ko wallafa bayanai a shafin ka, kawai sai ka shiga cikin taskan ka na ZamaniWeb ta hanyar amfani da lakabi da kalman sirrin da ka yi rajista da su, sai ka zabi "Shiga sashin sarrafa shafin".


Kasidu Masu Alaka