Ya Tsare-Tsaren ZamaniWeb Su ke?

Wallafan October 15, 2019. 3:14pm. Na Ahmad Bala. A Sashin Labaran ZamaniWeb

Manhajar mu na bai wa kowa daman mallakan shafin yanar gizo a kyauta, ba tare da biyan ko kwabo ba. Kuma shafin na kyauta yana zuwa tare da adireshin shafi na {dot}zamaniweb{dot}com. Sai dai wannan shafi na kyauta yana da wasu iyakoki. Muna bayar da shafin na kyauta ne domin baku daman yin gwaji da kuma koyon sarrafa shafin ku kawai. Abin da ya fi dacewa shi ne: bayan kirkiran shafin ku a kyauta, sai ku shiga tsarin mu na biya.

http://zamaniweb.com/administrator/files/19/10/1/tsare-tsaren-zamaniweb-com.png

Tsarin na biya zai baku daman samun kasaitaccen shafin yanar gizo wanda za ku iya sanya wa adireshi mai babban take (.com, .com.ng, da sauran su). Haka kuma a tsarin na biya ne za ku samu daman sanya dukkan nau'ukan 'Ad codes' don samun kudi a shafin ku. Sannan kuma shafin ku zai samu daman shiga Google a saukake domin akwai aiyukan SEO na musamman da muke yi ga shafukan da ke kan tsarin mu na biya. Bugu da kari! Akwai dama ta musamman don hada shafin ku da Youtube kai tsaye, ta yadda za ku iya wallafa bidiyoyin ku na Youtube a shafin ku cikin sauki. Akwai tarin aiyuka na morewa wadanda muka tanadar duk dai ga shafukan da ke kan tsarukan mu na biya.

Farashin tsari na biya yana farawa ne daga N1,300 kacal a wata, ko kuma N15,000 a shekara. Akwai kuma tsarin mu na "Babban Shafi" wanda ya fi dacewa da manyan mutane, ko manyan kamfanoni ko kungiyoyi da masana'antu.

Domin sanin yadda dukkanin farashi da tsare-tsaren mu suke a halin yanzu, ku shiga https://zamaniweb.com/farashi-da-tsare-tsare


Tura wannan zuwa:

Kasance na farko wajen yin sharhi a kan "Ya Tsare-Tsaren ZamaniWeb Su ke?"

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Game Da ZamaniWeb

ZamaniWeb manhajar yanar gizo ne da ke bayar da daman kirkiran shafin yanar gizo a harshen Hausa, cikin sauki. Za ku iya kirkiran shafin yanar gizo ko kuma blog kaman wannan a ZamaniWeb.com domin amfanin al\'ummar ku ko kuma domin bunkasa harkokin kasuwancin ku a zamanance. Ku ziyarci www.zamaniweb.com a yanzu domin mallakan naku shafin yanar gizon a kyauta!


Amfani da ZamaniWeb babu wahala!

Amfani da manhajar yanar gizon ZamaniWeb abu ne mai sauki. A duk lokacin da ka bukaci gudanar da gyare-gyare ko wallafa bayanai a shafin ka, kawai sai ka shiga cikin taskan ka na ZamaniWeb ta hanyar amfani da lakabi da kalman sirrin da ka yi rajista da su, sai ka zabi "Shiga sashin sarrafa shafin".


Kasidu Masu Alaka