Yadda Ake Canja Hotunan Shafi a ZamaniWeb

Wallafan June 29, 2018. 10:13pm. Na Ahmad Bala. A Sashin Darussan ZamaniWeb

A lokacin da ka kirkiri sabon shafin yanar gizon ka, idan ka ziyarci shafin za ka ga akwai wasu hotuna da muka saka a matsayin sumfur wato mun saka wadannan hotunan ne kawai domin mu nuna maka inda hotunan ka za su kasnace idan ka dora. Don haka sai ka je ka canja hotunan, ka dora naka hotunana wadanda suka danganci aiyukan shafin ka. Domin canja hotunan, sai ka shiga taskan ka, ka shiga sashin sarrafa shafin naka , sai ka latsa "Canja Hotunan Shafi". Idan daman nau'in shafin ka na kasuwanci ne ko na kungiya, to za ka ga hotuna hudu ne za ka bukaci canjawan kaman haka:

  • Hoton bango
  • Hoto na farko
  • Hoto na biyu
  • Hoto na uku

Yadda Ake Canja Hoton Bangon Shafi

Shi Hoton bango shi ne hoton da ke sama a shafin ka, kuma a kan sa ne taken shafin zai kasance. Domin canja hoton bangon, bayan ka budo bangaren "Canja Hotunan Shafi" za ka ga taken "Canja Hoton Bangon Shafi" a farko. Sannan za ka ga hoton da ke kai a halin yanzu. To kana da zabi guda biyu a nan:

  • Ko dai ka zabi hoto daga cikin jerin hotunan mu.
  • Ko kuma ka dora naka hoton kai tsaye wato ka yi "Upload".

Idan ka na so ka zabi hoton ne daga cikin jerin hotunan mu, to sai ka latsa wajen da aka ce "Zabi Hoto daga jerin hotunan mu" domin zaban hoton da ka ke so ya hau shafin ka a matsayin hoton bango.

Idan kuma ka na so ka dora na ka hoton ne wato "upload", sai ka yi kasa kadan za ka ga wajen da za ka taba don dauko hoto daga kwamfutar ka ko wayar ka, sai ka latsa "Dora hoton".

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/06/1/zw-doc31.png

Gargadi: A tabbata cewa fadin hoton ya kasance tsakanin 820px zuwa 1500px. Sannan tsayin sa kuma kada ya zarce 600px.

Ana iya amfani da kowane "Image Editor" domin yin "resize" din hoton zuwa tsayin da kuma fadin da ake bukata kafin a dora.

Yadda Ake Canja Sauran Hotunan Shafin

Idan ka latsa "Canja Hotunan Shafi" bayan ya bude, sai ka yi kasa, wato ka wuce wajen canja hoton bango. Za ka ga inda aka sa taken "Canja Hoto na farko". Sannan za ka ga hoton da ke kai a halin yanzu. Sannan kuma za ka ga wajen da za ka taba don dauko hoto daga kwamfutar ka ko wayar ka , sannan ka latsa "Dora hoton".

Haka ma za ka yi domin canja hoto na biyu da na ukun.


Tura wannan zuwa:

Kasance na farko wajen yin sharhi a kan "Yadda Ake Canja Hotunan Shafi a ZamaniWeb"

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Game Da ZamaniWeb

ZamaniWeb manhajar yanar gizo ne da ke bayar da daman kirkiran shafin yanar gizo a harshen Hausa, cikin sauki. Za ku iya kirkiran shafin yanar gizo ko kuma blog kaman wannan a ZamaniWeb.com domin amfanin al\'ummar ku ko kuma domin bunkasa harkokin kasuwancin ku a zamanance. Ku ziyarci www.zamaniweb.com a yanzu domin mallakan naku shafin yanar gizon a kyauta!


Amfani da ZamaniWeb babu wahala!

Amfani da manhajar yanar gizon ZamaniWeb abu ne mai sauki. A duk lokacin da ka bukaci gudanar da gyare-gyare ko wallafa bayanai a shafin ka, kawai sai ka shiga cikin taskan ka na ZamaniWeb ta hanyar amfani da lakabi da kalman sirrin da ka yi rajista da su, sai ka zabi "Shiga sashin sarrafa shafin".


Kasidu Masu Alaka