Ko ka san cewan za ka iya canja launin shafin ka wato "theme colour" a cikin kasa da minti daya?
Ga yanda abin ya ke:
A lokacin da ka kirkiri sabon shafin ka idan ka ziyarci shafin , za ka ga jimillan launin shafin shi ne baki ("black theme"). To za ka iya canja jimillan launin shafin zuwa kalan da ya dace da kasuwancin ka ko kalan kamfanin ka, cikin sauki ta hanyar zaba daga cikin jerin kalolin da muka tanadar. Domin canja launin shafin sai ka shiga taskan ka na ZamaniWeb, sai ka shiga sashin sarrafa shafin ka, sai ka latsa "Canja Launin Shafi". Idan ya budo, za ka ga jerin launuka, wato kalolin da za ka iya zaba. Sai ka zabi kalan da ka ke so ta hanyar latsa shi, sannan sai ka yi kasa, ka latsa maballin "Sabunta Saitin Launin".

Shi ke nan!