Yadda Ake Gyara Bayanan Shafi a ZamaniWeb

Wallafan June 10, 2018. 6:45pm. Na Ahmad Bala. A Sashin Darussan ZamaniWeb

Abu na farko kuma mafi muhimmanci da ya kamata a gaggauta yi bayan an kirkiri sabon shafin ZamaniWeb shi ne gyara bayanan shafin. Bayanan shafin su ne kaman haka:

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/06/1/zw-doc4.png

(1) Taken shafin

Wannan shi ne babban taken shafin wanda zai bayyana a saman shafin, kuma shi ne taken da zai bayyana a yayin da aka binciko shafin ka a shafukan bincike-bincike irin su Google. Taken shafin shi ne abu mafi muhimmanci a shafin. A yi kokari a takaita shi kada ya zarce ruraben haruffa 70.

(2) Takaitaccen bayani game da shafin

Wannan shi ne dan gajeren bayani game da shafin ka ko manufan shafin gaba daya, a dunkule. Wannan bayanin na da matukar muhimmanci a shafin yanar gizon ka, domin shi ne zai bayyana a karkashin taken shafin ka idan aka tura adireshin shafin a zaurukan zumunta irin su Facebook da WhatsApp. Kuma zai bayyana a karkashin taken shafin a yayin da wani ya binciko shafin ka a shafukan bincike-bincike irin su Google.

(3) Takaitaccen gabatarwan shafin

Wannan shi ne dan takaitaccen sako wanda zai kasance a matsayin gabatarwan shafin. Zai iya kasancewa wani dan sako ne da ka ke maziyarta shafin su fara gani a yayin da suka budo shafin farko na shafin. Shi wannan zai bayyana ne a karkashin kan shafin, cikin rubutu mai kauri.

(4) Taken bayani na farko

Wannan shi ne taken duk wani bayani da ka zabi ka sanya a matsayin bayani ko sako na rukunin farko a na bayanan da ke tsakiya a shafin farko na shafin yanar gizon ka. Zai bayyana ne a saman hoto na farko a shafin.

(5) Bayanin na farko

Wannan shi ne duk wani bayani ko sako da ka zabi ka sanya a matsayin bayanin da ke rukunin farko na byanan da ke tsakiya a shafin farko na shafin yanar gizon ka. Zai bayyana ne a a karkashin hoto na farko a shafin.

(6) Taken bayani na biyu

Wannan shi ne taken duk wani bayani da ka zabi ka sanya a matsayin bayani ko sako na rukunin na biyu a bayanan da ke tsakiya a shafin farko na shafin yanar gizon ka. Zai bayyana ne a saman hoto na biyu a shafin.

(7) Bayanin na biyu

Wannan shi ne duk wani bayani ko sako da ka zabi ka sanya a matsayin bayanin da ke rukuni na biyu na byanan da ke tsakiya a shafin farko na shafin yanar gizon ka. Zai bayyana ne a a karkashin hoto na biyu a shafin.

(8) Taken bayani na uku

Wannan shi ne taken duk wani bayani da ka zabi ka sanya a matsayin bayani ko sako na rukuni na uku a bayanan da ke tsakiya a shafin farko na shafin yanar gizon ka. Zai bayyana ne a saman hoto na uku a shafin.

(9) Bayanin na uku

Wannan shi ne duk wani bayani ko sako da ka zabi ka sanya a matsayin bayanin da ke rukuni na uku na bayanan da ke tsakiya a shafin farko na shafin yanar gizon ka. Zai bayyana ne a a karkashin hoto na uku a shafin.

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/06/1/zw-doc6.png

(10) Taken muhimmin sako na shafin

Wannan shi ne taken duk abin da ka zabi ka sanya a matsayin muhimmin sako wanda zai bayyana a bangaren kasan shafin.

(11) Muhimmin sakon shafin

Wannan shi ne wani dan muhimmin bayani da ka ke son maziyarta shafin ka su gani a kasan shafin. Wato abin da ake ce ma "Call to action" a turance. Zai iya kasancewa adireshin ofishin ka ne ko adireshin wurin kasuwancin ka tare da lambobin waya na kamfanin ka ko kasuwancin ka, ko kuma duk wani "kira" da ka ke son ka yi ga wanda ya ziyarci shafin naka.

(12) Kalaman karshe

Wannan shi ne wani dan kalma ko kalaman karshe da ka ke son sakawa a karshen shafin ka. Kaman "Na gode da kuka ziyarci wannan shafi nawa" ko kuma "Ku biyo ni a zaurukan sada zumunta" da dai abubuwa makamantan wadannan.

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/06/1/zw-doc7.png

A tabbata an latsa maballin "Sabunta bayanan" da ke kasa, bayan an kammala rubuta bayanan, domin adanawa.


Tura wannan zuwa:

Kasance na farko wajen yin sharhi a kan "Yadda Ake Gyara Bayanan Shafi a ZamaniWeb"

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Game Da ZamaniWeb

ZamaniWeb manhajar yanar gizo ne da ke bayar da daman kirkiran shafin yanar gizo a harshen Hausa, cikin sauki. Za ku iya kirkiran shafin yanar gizo ko kuma blog kaman wannan a ZamaniWeb.com domin amfanin al\'ummar ku ko kuma domin bunkasa harkokin kasuwancin ku a zamanance. Ku ziyarci www.zamaniweb.com a yanzu domin mallakan naku shafin yanar gizon a kyauta!


Amfani da ZamaniWeb babu wahala!

Amfani da manhajar yanar gizon ZamaniWeb abu ne mai sauki. A duk lokacin da ka bukaci gudanar da gyare-gyare ko wallafa bayanai a shafin ka, kawai sai ka shiga cikin taskan ka na ZamaniWeb ta hanyar amfani da lakabi da kalman sirrin da ka yi rajista da su, sai ka zabi "Shiga sashin sarrafa shafin".


Kasidu Masu Alaka