Yadda Ake Kirkiran Sabon Sashe Na Blog a ZamaniWeb

Wallafan August 10, 2018. 12:11pm. Na Ahmad Bala. A Sashin Darussan ZamaniWeb

Da farko, idan sabon shafi ne, dole sai ka fara da kirkiran sashe ('category') sannan za ka samu daman wallafa kasidan ka na farko a shafin.

Domin kirkiran sabon sashe, sai ka shiga taskan ka na ZamaniWeb, ka shiga bangaren gudanarwan shafin wato bangaren sarrafa shafin, sai ka zabi "Kirkiri Sabon Sashe". Zai budo maka wajen da za ka rubuta Sunan Sashen, sannan sai ka latsa maballin "Kirkiri Sashe" da ke kasa, domin kaddamar da sabon sashen. Sunan sashen zai iya kasancewa kalma daya ko kuma jerin kalmomi, kuma za a iya bada tazara a tsakanin kalmomin. Sunan sashen zai iya kunsan haruffa da lambobi da kuma alaman "-". Amma ba zai iya kunsan sauran alamomin rubutu ba, irin su aya da wakafi da alaman tambaya. Babu iyaka a kan adadin sashen da za ka iya kirkira a ZamaniWeb. Kuma daga lokacin da ka kirkiri sashe guda a shafin ka na ZamaniWeb to za ka iya wallafa kasidu ko guda nawa ne a karkashin sashen.

Karin Bayani Game Da Sassan blog a ZamaniWeb

  • Babu iyaka a kan adadin sashen da za ka iya kirkira a ZamaniWeb.
  • Daga lokacin da ka kirkiri sashe guda a shafin ka na ZamaniWeb to za ka iya wallafa kasidu ko guda nawa ne a karkashin sashen.
  • Za ka iya gyara sunan sashen da ka kirkira ta hanyar latsa bangaren "Gyara Sassa" da ke farfajiyar sarrafa shafin ka.
  • Haka kuma za ka iya goge sashen da ka kirkira ta hanyar latsa bangaren "Goge Sashe" da ke farfajiyar gudanarwan shafin ka.
  • Sai dai a yi hattara yayin goge sashe, domin goge sashen zai hada da goge duk wani kasida da aka wallafa ko aka adana a karkashin sashen. Don haka sai a tabbatar cewan babu kasidu a sashen da ake bukatan gogewan kafin a goge.

Tura wannan zuwa:

An yi sharhi 2 a kan "Yadda Ake Kirkiran Sabon Sashe Na Blog a ZamaniWeb"


Babu hoto31-08-2018
arewasong

wakoki


Babu hoto01-05-2019
abdulhamid

Rubuta sharhin a nan...sirrin-azuma

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Game Da ZamaniWeb

ZamaniWeb manhajar yanar gizo ne da ke bayar da daman kirkiran shafin yanar gizo a harshen Hausa, cikin sauki. Za ku iya kirkiran shafin yanar gizo ko kuma blog kaman wannan a ZamaniWeb.com domin amfanin al\'ummar ku ko kuma domin bunkasa harkokin kasuwancin ku a zamanance. Ku ziyarci www.zamaniweb.com a yanzu domin mallakan naku shafin yanar gizon a kyauta!


Amfani da ZamaniWeb babu wahala!

Amfani da manhajar yanar gizon ZamaniWeb abu ne mai sauki. A duk lokacin da ka bukaci gudanar da gyare-gyare ko wallafa bayanai a shafin ka, kawai sai ka shiga cikin taskan ka na ZamaniWeb ta hanyar amfani da lakabi da kalman sirrin da ka yi rajista da su, sai ka zabi "Shiga sashin sarrafa shafin".


Kasidu Masu Alaka