Yadda Ake Wallafa a Blog Na ZamaniWeb

Wallafan September 16, 2018. 12:22pm. Na Ahmad Bala. A Sashin Darussan ZamaniWeb

Wannan bayani ne cikakke game da yanda za a wallafa kasida ('post') a blog na ZananiWeb.

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/09/1/zw-wallafa-kasida-3.png

Da farko, idan sabon shafi ne, dole sai ka fara da kirkiran sashe ('category') sannan za ka samu daman wallafa kasidan ka na farko a shafin.

Yadda Ake Kirkiran Sabon Sashe Na Blog ("Category") a ZamaniWeb

Domin kirkiran sabon sashe, sai ka shiga taskan ka na ZamaniWeb, ka shiga bangaren gudanarwan shafin wato farfajiyar sarrafa shafin, sai ka zabi "Kirkiri Sabon Sashe". Zai budo maka wajen da za ka rubuta Sunan Sashen, sannan sai ka latsa maballin "Kirkiri Sashe" da ke kasa, domin kaddamar da sabon sashen. Sunan sashen zai iya kasancewa kalma daya ko kuma jerin kalmomi, kuma za a iya bada tazara a tsakanin kalmomin. Sunan sashen zai iya kunsan haruffa da lambobi da kuma alaman "-". Amma ba zai iya kunsan sauran alamomin rubutu ba, irin su aya da wakafi da alaman tambaya.

Karin Bayani Game Da Sassan blog a ZamaniWeb

  • Babu iyaka a kan adadin sashen da za ka iya kirkira a ZamaniWeb.
  • Daga lokacin da ka kirkiri sashe guda a shafin ka na ZamaniWeb to za ka iya wallafa kasidu ko guda nawa ne a karkashin sashen.
  • Za ka iya gyara sunan sashen da ka kirkira ta hanyar latsa bangaren "Gyara Sassa" da ke farfajiyar sarrafa shafin ka.
  • Haka kuma za ka iya goge sashen da ka kirkira ta hanyar latsa bangaren "Goge Sashe" da ke farfajiyar gudanarwan shafin ka.
  • Sai dai a yi hattara yayin goge sashe, domin goge sashen zai hada da goge duk wani kasida da aka wallafa ko aka adana a karkashin sashen. Don haka sai a tabbatar cewan babu kasidu a sashen da ake bukatan gogewan kafin a goge.

Yadda Za a Wallafa Sabon Kasida ("Post") Na Blog a ZamaniWeb

Domin wallafa sabon kasida wato 'post' a shafin ka na ZamaniWeb, bayan ka shiga farfajiyar sarrafa shafin ka, zaka ga wajen da aka sa "Wallafa Kasida" sai ka latsa shi, zai budo maka shafin wallafan inda zaka ga guraben cikewa kaman haka:

  • Zabi Sashe
  • Taken Kasidan
  • Kasidan
  • Bayanin Kasidan

To a gurbi na farko wato "Zabi Sashe" idan ka taba shi zai jero maka sassan da ka kirkira, to sai ka zabi sashen da kake son sabon kasidan ya kasance a ciki.

Sai kuma gurbi na biyu wato "Taken Kasidan" inda a nan ne za ka rubuta taken kasidan da kake son wallafawa.

Sai kuma gurbi na uku wato "Kasidan" wanda shi ne gangan jikin kasidan, a nan ne za ka rubuta ainahin abin da kasidan ya kunsa. A nan za ka iya yin sakin layi a cikin rubutun ka ta hanyar latsa alamar 'Enter' na madannan kwamfuta ko wayar ka. Sannan kuma za ka iya yin sakin layi ta hanyar amfani da alamomin BBcode na 'paragraph' kaman haka:

[ p ] Rubutu a tsakani... [ / p ]
ko kuma ta hanyar amfani da alamomin HTML na 'paragraph' kaman haka:
< p > Rubutu a tsakani... < / p >

A gangan jikin kasidar ka za ka iya amfani da kusan dukkan alamomin sarrafa rubutu na BBcode da HTML don sarrafa rubutun ka yadda kake so.

Sai kuma gurbi na hudu wato "Bayanin kasidan" inda za ka rubuta dan takaitaccen bayani game da kasidan. A nan ana so ne ka rubuta abin da kasidan ke magana a kai ko kuma manufan kasidan ko kuma duk wani sako da kake ganin zai iya janyo ra'ayin maziyarta zuwa ga karanta kasidan. Za a iya barin gurbin bayanin kasidan babu komai, amma sanya shi na da matukan muhimmanci, domin shi ne zai bayyana a karkashin taken kasidan idan maziyarta shafin ka suka yi 'sharing' wato suka tura kasidan ka zuwa zaurukan zumunta irin su Facebook da WhatsApp. Kuma wannan bayanin kasidan shi ne zai bayyana a karkashin taken kasidan a cikin jerin sakamakon bincike na shafukan bincike-bincike irin su Google.

Idan an kammala cike guraben sai a latsa koren maballin "Wallafa | Adana" da ke kasa domin wallafa kasidan kai tsaye.

Yadda Ake Adana Kasida Idan Ba a So a Wallafa Yanzu

A karkashin guraben cikewan nan za ku ga wani dan karamin akwatin latsawa wato "check box" tare da rubutu a gaban sa da ke cewa: "Ba na so a wallafa yanzu. Saka a rumbun adana". To idan ba ka so ka wallafa kasidan a nan take sai ka latsa wannan akwatin, za ka ga ya fito da alaman maki, wanda ke nuna cewan za a adana kasidan ne ba wallafawa ba. Bayan ka yi hakan sai ka latsa koren maballin "Wallafa | Adana" da ke kasa domin adanawan.

Duk kasidan da ka yi wa hakan ba zai bayyana a shafin ka ba. Za ka gan shi a bangaren "Sarrafa kasidu" na farfajiyar sarrafa shafin ka tare da alaman "An adana".

A duk lokacin da ka bukaci yin gyara ko kuma wallafa kasidan da ka adana sai ka shiga bangaren "Sarrafa kasidu" da ke farfajiyar sarrafa shafin ka. Sai ka latsa "Gyara" a jikin kasidan da ka adana din wanda daga nan za ka samu daman gyarawan da kuma wallafawan ko kuma sake adanawa.

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/09/1/zw-wallafa-kasida-2.png


Tura wannan zuwa:

An yi sharhi 5 a kan "Yadda Ake Wallafa a Blog Na ZamaniWeb"


Babu hoto23-01-2019
Aliyu Suleiman lawal

Siyasa ra ayi che


Babu hoto14-07-2019
kabir Muhammad

kabir@blogs.com


Babu hoto16-08-2019
HARUN

Rubuta sharhin a nan...BANSAMU GAMSUWABA WANAN NAN SAFIN


Babu hoto21-08-2019
FIKKIRA

Rubuta sharhin a nan BAKUMAI


Babu hoto13-09-2020
Yayi

MASHA ALLAH

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Game Da ZamaniWeb

ZamaniWeb manhajar yanar gizo ne da ke bayar da daman kirkiran shafin yanar gizo a harshen Hausa, cikin sauki. Za ku iya kirkiran shafin yanar gizo ko kuma blog kaman wannan a ZamaniWeb.com domin amfanin al\'ummar ku ko kuma domin bunkasa harkokin kasuwancin ku a zamanance. Ku ziyarci www.zamaniweb.com a yanzu domin mallakan naku shafin yanar gizon a kyauta!


Amfani da ZamaniWeb babu wahala!

Amfani da manhajar yanar gizon ZamaniWeb abu ne mai sauki. A duk lokacin da ka bukaci gudanar da gyare-gyare ko wallafa bayanai a shafin ka, kawai sai ka shiga cikin taskan ka na ZamaniWeb ta hanyar amfani da lakabi da kalman sirrin da ka yi rajista da su, sai ka zabi "Shiga sashin sarrafa shafin".


Kasidu Masu Alaka