Yadda Za a Kirkiri Sabon Shafin Yanar Gizo a ZamaniWeb

Wallafan March 11, 2018. 3:30pm. Na Ahmad Bala. A Sashin Darussan ZamaniWeb

Ga cikakken bayani kan yadda za ku kirkiri sabon shafin yanar gizon ku a ZamaniWeb.com cikin matakai 4

http://zamaniweb.com/administrator/files/18/03/1/kirkiri_shafin_yanzu!.png

1. Yin Rajista (Bude Sabon Taska)

A matakin farko, dole sai ka fara yin rajista na sabon taska wato "New Account Registration" kenan a turance. Yin rajistan sabon taskan kyauta ne kuma galibi bai wuce mintuna 2-3 ba. Ana yin rajistan ne ta hanyar shiga shafin yin rajistan, wato idan ka budo shafin farko na ZamaniWeb (zamaniweb.com) sai ka latsa maballin da ke cewa "Yi Rajista". Ko kuma kai tsaye, ana iya bin https://zamaniweb.com/administrator/shafin-rajista
http://zamaniweb.com/administrator/files/18/03/1/yi-rajista-img.png
A shafin yin rajistan za a ga fom mai guraben cikewa kamar haka:
*Lakabi (wato username)
*Cikakken Suna
*Jinsi
*Ranar Haihuwa
*Kasa
*Adireshin Email
*Lambar waya
*Kalman Sirri (wato password)
*Maimaita kalman sirri
*Amincewa da dokoki da ka'idojin ZamaniWeb

Wajibi ne a cike kowane gurbi da ke fom din sannan a latsa maballin "Aika bukatan yin rajistan" da ke kasan fom din. Idan an samu nasaran yin rajistan, za a ga sakon "barka" ya bayyana a saman shafin wanda ke nuna cewa rajistan ya kammalu kuma sabon taskan ya budu. Daga nan sai a je zuwa mataki na gaba wanda shi ne tantance adireshin Email.

2. Tantance Adireshin Email

Wajibi ne sai mai rajista ya tantance adireshin Email din da ya yi rajistan da shi, ta hanyar latsa mahada ("link") da ke cikin sakon Email din da manhajar mu ya aika ma sa kai tsaye zuwa "Inbox" na adireshin Email din sa a lokacin da ya kammala rajistan. Don haka bayan mutum ya kammala yin rajistan kaman yadda mu ka fado a mataki na farko, to sai ya je ya duba cikin sakonnin Email din sa, zai ga sabon sako daga ZamaniWeb, sai ya bude sakon, a cikin sakon zai ga mahadan tantancewan ("verification link") sai ya latsa shi. Idan ya latsa mahadan zai ga shafin ZamaniWeb ya budo tare da wani sanarwan da ke nuni da cewan an tantance adireshin Email din. Shi ke nan! Rajistan ya kammalu, daga nan zai iya shiga cikin taskan a ko da yaushe don gudanar da harkokin shafi.

3. Shiga Taska (LogIn)

Shiga cikin taska wanda a turance a kan ce "Account login" ko "Sign in" shi zai ba ka daman cin moriyar dukkan bangarorin ZamaniWeb, kaman bangaren kirkiran sabon shafin yanar gizo da bangaren sarrafa shafukan yanar gizon da ka kirkira da dai sauran su. Domin shiga cikin taskan ka na ZamaniWeb a ko da yaushe sai ka latsa maballin "Shiga Taska" wanda ke shafin farko na ZamaniWeb ko kuma kai tsaye ana iya bin https://zamaniweb.com/administrator/shafin-shiga
http://zamaniweb.com/administrator/files/18/03/1/shiga-taska-img.png
A shafin shiga taskan za a ga wani dan gajeren fom mai guraben cikewa guda biyu kamar haka:
*Lakabi
*Kalman Sirri
Sai a rubuta lakabin da aka yi rajistan taskan da shi a gurbin lakabin. Sannan kuma a rubuta kalman sirrin da aka yi rajistan taskan da shi a gurbin kalman sirrin. Sannan sai a latsa maballin "Shiga da ni ciki" da ke kasan fom din.

4. Kirkiran Sabon Shafin Yanar Gizo

Bayan shiga taskan, kai tsaye, za a fado bangaren "Gudanarwan shafin" wato "Administrator dashboard" kenan a turance. A nan ne za a samu daman kirkiran sabon shafin yanar gizo, da kuma daman shiga bangaren sarrafa shafukan yanar gizon. A shigowa na farko, za a ga wani sanarwa a sama mai nuni da cewan ba ka kirkiri wani shafi ba a halin yanzu, kuma idan ka yi, jerin shafukan da ka kirkira zai baiyana a nan. A kasa da wannan za a ga wani fom mai taken "Kirkiri Shafin Yanar gizon Ka" ko "Kirkiri Shafin Yanar gizon Ki". Wannan fom shi ne za a cike domin kirkiran sabon shafin yanar gizo a ZamaniWeb. Wannan fom na da guraben cikewa guda hudu kamar haka:
*Taken Adireshin Shafin
*Taken Shafin
*Nau'in Shafin
*Yaren Shafin
http://zamaniweb.com/administrator/files/18/03/1/kirkiri-shafi-img.png

To a gurbi na farko, wato "Taken adireshin shafi" za ka rubuta kalma ne wanda ka ke son ya kasance a cikin adireshin shafin da za ka kirkira. Misali: Idan kana so taken adireshin ya kasance www{dot}wasanni{dot}zamaniweb{dot}com ne to sai ka rubuta "wasanni" a gurbin na taken adireshin shafin. Kalman kadai za ka rubuta. Idan ma sunan ka ka ke son ya fito a cikin taken adireshin, to sunan kadai za ka rubuta, misali "Adam". Ba a bada tazara wajen rubuta kalman na taken adireshin shafin kuma ba a sanya alamomin rubutu irin su aya da wakafi, amma za ka iya amfani da alaman "-" idan kana bukata. Kada kalman ya wuce guraben haruffa 20.

Sai gurbi na biyu, wato "Taken Shafi". Wannan shi ne ainahin sunan shafin ko kuma taken shafin. Za ka rubuta ainahin taken shafin ne ko kuma duk wani rubutu da ka ke son ya kasance a saman shafin da za ka kirkira. Taken shafin ka shi ne abu na farko da maziyarta shafin ka za su gani a saman shafin. Shi wannan "taken shafi" ba daya ya ke da "taken adireshin shafi" ba. Taken shafin zai iya kasancewa kalma daya ko kuma jerin kalmomi. Za ka iya amfani da alamomin rubutu kuma za ka iya bada tazara yayin rubuta taken shafin.

Gurbi na uku kuwa, wato "Nau'in Shafi" kana taba shi zai jero maka abubuwan zabi. Sai ka zabi nau'in shafin da ka ke son kirkira. Misali, idan shafin na kasuwanci ka ke son kirkira, to sai ka tabbatar ka zabi "Na kasuwanci" a nan wajen.

Gurbi na hudu kuma, wato "Yaren Shafi" shi ma da ka taba zai jero maka abubuwan zabi, sai ka zaba. Misali, idan shafin turanci ka ke son ka kirkira, to sai ka tabbatar ka zabi "English" a nan wajen.


Tura wannan zuwa:

An yi sharhi 2 a kan "Yadda Za a Kirkiri Sabon Shafin Yanar Gizo a ZamaniWeb"


Babu hoto26-03-2018
Ahmad Musa Kaura Namoda

Don allah ina bukatar karin bayani dangane da yadda zan kirkiri nawa sabon shafi kuma ina so a turo min da misalai na yadda zan cike guraben


Babu hoto17-08-2019
Amiiru liman

Al'ihsaan.com

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Game Da ZamaniWeb

ZamaniWeb manhajar yanar gizo ne da ke bayar da daman kirkiran shafin yanar gizo a harshen Hausa, cikin sauki. Za ku iya kirkiran shafin yanar gizo ko kuma blog kaman wannan a ZamaniWeb.com domin amfanin al\'ummar ku ko kuma domin bunkasa harkokin kasuwancin ku a zamanance. Ku ziyarci www.zamaniweb.com a yanzu domin mallakan naku shafin yanar gizon a kyauta!


Amfani da ZamaniWeb babu wahala!

Amfani da manhajar yanar gizon ZamaniWeb abu ne mai sauki. A duk lokacin da ka bukaci gudanar da gyare-gyare ko wallafa bayanai a shafin ka, kawai sai ka shiga cikin taskan ka na ZamaniWeb ta hanyar amfani da lakabi da kalman sirrin da ka yi rajista da su, sai ka zabi "Shiga sashin sarrafa shafin".


Kasidu Masu Alaka