ZamaniWeb Ya Samu Nasara a Gasar Click-On Kaduna KAD-DIP 2019

Wallafan December 22, 2019. 2:38pm. Na Ahmad Bala. A Sashin Labaran ZamaniWeb

http://zamaniweb.com/administrator/files/19/12/1/zw-logo.png

ZamaniWeb ya samu nasarar zama daya daga cikin kamfanoni 30 da aka zaba a cikin shirin Click-On Kaduna Digital Entrepreneurship Program wanda shiri ne da gwamnatin jihar Kaduna ta kirkiro tare da hadin gwiwar World Bank da Rockefella Foundation da kuma Ventures Platform, da manufan bunkasa kamfanoni masu tasowa a fannin fasahar sadarwan zamani.

http://zamaniweb.com/administrator/files/19/12/1/ahmad-bala-pitching.jpg

Wannan nasarar ta samu ne bayan gagarumin gasar gabatar da jawabi game da kamfanoni da aka gudanar tsakanin jagororin kamfanonin guda 180 a watan nuwamban da ta gabata na wannan shekara ta 2019. Jagoran ZamaniWeb, Ahmad Bala ne ya gabatar da jawabi game da ZamaniWeb a gasar. Inda bayan an kammala, alkalan gasar suka fitar da kamfanoni guda 30 a matsayin wadanda suka samu nasara a gasar, ciki har da ZamaniWeb.

A karshe an gabatar da kyaututtuka da karin horaswa na musamman wato "Incubation program" na tsawon wata guda ga jagororin kamfanonin da suka samu nasarar.

http://zamaniweb.com/administrator/files/19/12/1/kaddip2019-pitch-competition-winners.jpg

A gare mu, wannan nasarar na nufin samun ci gaba ne a kokarin da muke yi na ganin wannan manhaja na ZamaniWeb ya bunkasa.

http://zamaniweb.com/administrator/files/19/12/1/ahmad-bala-with-world-bank-country-director.jpg

"Wannan ba nasara ce gare mu kadai ba. Nasara ce ga al'ummar Arewa, da Najeriya baki daya, da ma Afrika baki daya, musamman ma'abota amfani da harshen Hausa, kasancewar ZamaniWeb shi ne manhajar yanargizo irin sa na farko da aka gina shi cikin daya daga cikin manyan harsunan Afrika wato Hausa. Muna farin ciki kwarai, kuma da yardan Allah za mu ci gaba da kokari don ganin mun kai ZamaniWeb mataki na gaba. Hakika aiki ne mai wahala, amma da yardan Allah za mu iya! Muna godiya da ci gaba da amincewa da mu da kuke yi da kuma kwarin gwiwar da kuke kara ba mu."
- Ahmad Bala


Tura wannan zuwa:

An yi sharhi 1 a kan "ZamaniWeb Ya Samu Nasara a Gasar Click-On Kaduna KAD-DIP 2019"


Babu hoto07-06-2020
Benzene

Masha Allah farin ciki

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Tantancewa:
hoton CAPTCHA

Game Da ZamaniWeb

ZamaniWeb manhajar yanar gizo ne da ke bayar da daman kirkiran shafin yanar gizo a harshen Hausa, cikin sauki. Za ku iya kirkiran shafin yanar gizo ko kuma blog kaman wannan a ZamaniWeb.com domin amfanin al\'ummar ku ko kuma domin bunkasa harkokin kasuwancin ku a zamanance. Ku ziyarci www.zamaniweb.com a yanzu domin mallakan naku shafin yanar gizon a kyauta!


Amfani da ZamaniWeb babu wahala!

Amfani da manhajar yanar gizon ZamaniWeb abu ne mai sauki. A duk lokacin da ka bukaci gudanar da gyare-gyare ko wallafa bayanai a shafin ka, kawai sai ka shiga cikin taskan ka na ZamaniWeb ta hanyar amfani da lakabi da kalman sirrin da ka yi rajista da su, sai ka zabi "Shiga sashin sarrafa shafin".


Kasidu Masu Alaka